CAF Zata Yanke Shawara Kan Gasar 2019, Bayan Zaben Kamaru
(last modified Fri, 28 Sep 2018 18:02:42 GMT )
Sep 28, 2018 18:02 UTC
  • CAF Zata Yanke Shawara Kan Gasar 2019, Bayan Zaben Kamaru

Hukumar kwallon kafa ta AFrika CAF, ta ce har yanzu bata yanke shawara ba kan gudanar da gasar cin kofin Afrika na 2019 a Jamhuriya Kamaru ba.

A wata hira da shafin lemonde.fr, shugaban hukumar , Ahmad Ahmad, ya ce har yanzu hukumar ta CAF bata tsaida magana ba, kuma ba zata yi magana ba yanzu kan ko zata gudanar da gasar ta 2019 a Kamaru ba ko kuma a'a.

Mista Ahmad, ya kara da cewa hukumar ba zata yi hakan ba, gabanin babban zaben kasar ta Kamaru ba, don kada hakan ya kawo cikas ga yakin neman zaben kasar da ake ciki.

A ranar 7 ga watan Oktoba mai zuwa ne al'ummar kasar ta Kamaru zasu kada kuri'a a zaben shugaban kasar. 

A yanzu haka dai kwamitin gudanarwa na hukumar ta CAF na taro a kasar Masar domin duba halin da ake ciki akan shirye shiryen gasar ta 2019.