An Yi Zanga Zanga Kan Yawaitar Hare Hare A Burkina Faso
(last modified Sun, 30 Sep 2018 11:05:37 GMT )
Sep 30, 2018 11:05 UTC
  • An Yi Zanga Zanga Kan Yawaitar Hare Hare A Burkina Faso

A Burkina Faso, daruruwan mutane ne suka shiga wata zanga zanga a jiya Asabar, a Ouagadugu babban birnin kasar, domin nema ga mahukuntan aksar su dau mataki kan yawaitar hare hare na mayakan dake ikirari da sunan jihadi a kasar.

Ko baya ga hakan masu zanga zangar sun nuna fishinsu kan batutuwan da suka shafi sha'anin tsaro a kasar, da ta'addanci da cin hanci da rashwa da kuma tsadar rayuwa.

Burkina faso dake raba iyaka da kasashen Mali, Nijar na fuskantar hare hare daga mayakan dake ikirari da sunan jihadi a farkon shekara 2015, inda aka kai hare hare har uku a Ouagadugu fadar mulkin kasar, baya wadanda ake kaiwa a arewaci da gabashin kasar.

Alkalumman da mahukuntan kasar suka fitar a tsakiyar watan Satumban nan sun nuna cewa, hare haren mayakan jihadi sun yi sanadin mutuwar mutane 118, da suka hada da fararen hula 70 da jami'an tsaro 48.