Bam Ya Kashe Sojojin Burkina Faso Akalla 6
Wani bam da aka dasa kan hanya ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji akalla shida, da kuma raunana wasu a gabashin Burkina Faso.
Wata majiyar tsaro ta shaidawa kamfanin dilancin labaren Faransa na AFP cewa, da safiyar yau Alhamis, wata motar sojoji ta taka wani bam kirar hannu a tsakanin hanyar garin Gayeri zuwa Futuri dake gabashin kasar.
Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan wani hari da aka kai a wani sansanin jami'an tsaro na jandarma a yankin Inata dake arewacin kasar.
Kasar Burkina Faso dake raba iyaka da kasashen Mali da Nijar, na fuskantar hare hare mayakan dake ikirari da sunan jihadi tun farkon shekara 2015.
Alkalumman da hukumomin kasar ta Burkina suka fitar a tsakiyar watan Satumba da ya gabata sun nuna cewa hare haren da ake kaiwa kasar sun yi sanadin mutuwar 118 da suka hada da fararen hula 70 da kuma jmai'an tsaro 48.