Masar: An Kama Dan Ta'adda Mafi Hatsari A Kasar Libya
(last modified Tue, 09 Oct 2018 06:44:10 GMT )
Oct 09, 2018 06:44 UTC
  • Masar: An Kama Dan Ta'adda Mafi Hatsari A Kasar Libya

Kakakin sojojin kasar Libya masu biyayya ga Halifa Haftar ya sanar da cewa sun kama dan ta'addar kasar Masar mafi hatsari a garin Derna a jiya Litinin.

Kakakin sojojin na Libya Ahma al-Mismari ya ce sun kame Hisham Ashmawy ne a wani harin da su ka kai a garin Derna.

Shi dai Hisham Ashmawy dan shekaru 39, shi ne kwamandan rundunar da ake kira Murabitun mai alaka da kungiyar alka'ida. Tun shekaru 4 da su ka gabata ne gwamnatin kasar Masar ta fara neman sa ruwa a jallo saboda hannun da yake da shi wajen kai hare-hare a kasar ta Masar.

A shekarar 2000 ne Ashamawy ya kammala karatu a jami'ar yaki ta kasar Masar sannan kuma ya sami horo na aikin soja a kasar Amurka.