Zimbabwe : An Haramta Zanga-zanga Kan Karin Haraji
Rundunar 'yan sanda a Zimbabwe, ta haramtawa kungiyoyin kwadago na kasar gudanar da zanga-zangar nuna adawa da karin haraji kan aikewa da kudade.
Wata sanarwa da rundunar 'yan sandan ta fitar a jiya, ta ce ba zai yuwu a gudanar da zanga-zangar ba, saboda har yanzu haramta taron jama'a da aka yi biyo bayan barkewar cutar amai da gudawa a kasar na nan daram.
A kwanan nan ne dai gwamnatin kasar ta sanar da karin haraji da kaso 2 bisa dari kan aikewa da kudi ta kafar intanet, lamarin da bai yi wa wasu 'yan kasar dadi ba.
Yau Laraba ne dai babbar kungiyar kwadago ta kasar, ta yi kira da a gudanar da zanga-zanga da nufin nuna adawa da karin harajin da ya haifar da karuwar farashin kayayyaki.
A makon da ya gabata ne Ministan kudi na kasar, Mthuli Ncube, ya sanar da karin, a matsayin wani mataki na samun karin kudin hidima wa al'ummar kasar, sai dai akasarin 'yan kasar ba su yi na'am da matakin ba, inda suke ganin dama can suna biyan harajin da wuce kima.