Uganda : Zaizayar Kasa Ta Yi Ajalin Mutum 7
(last modified Thu, 11 Oct 2018 19:05:01 GMT )
Oct 11, 2018 19:05 UTC
  • Uganda : Zaizayar Kasa Ta Yi Ajalin Mutum 7

Mutane 7 ne aka tabbatar da mutuwarsu sanadiyyar zaizayar kasa wacce ta biyu bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya a yau Alhamis a kasar Uganda.

Jaridar Punch ta Najeriya ta bayyana cewa mutane 7 ne suka rasa rayukansu a gabacin kasar Uganda sanadiyyar zaizayar kasa bayan mamakon ruwan sama da aka yi a yankin.

Labarin ya nakalto kakin kungiyar Red Cross a yankin Irene Nakasiita yana cewa mai yuwa yawan wadanda suka rasu ya karu don har yanzun basu kammala zagayawa zuwa ga yankunan da abin ya shafa ba.

Nakasiita ya kara da cewa mutane da dama sun kauracewa kidajensu don tsoron rubtawarsu. A halin yanzu ana ruwan sama sosai a yankin Bududa na gabacin kasar. Yankin Bududa yana kusa da dutsen Elgon na kan iyakar kasar da Kasar Kenya. Har'ila yau a shekara ta 2010 da kuma 2012 mutane kimani 100 ne suka rasa rayukansu sanadiyar zaizayewar kasa a yankin.