An Nada 'Yar Afrika Ta Farko A Matsayin Shugabar Kungiyar OIF
An nada Louise Mushikiwabo 'yar kasar Ruwanda a matsayin shugaban kungiyar kasashe masu magana da harshen faransanci "Francophone" a takaice.
Kamfanin dillancin labaran Associated Press ta bayyana cewa Louise Mushikiwabo ta shahara a fagen ayyukan diblomasiyya kafin ta sami wannan matsayin. Sannan ita ce macce ta farko da ta taba riki wannan matsayin.
Louise Mushikiwabo ta maye gurbin ouis Michaelle Jean wanda wa'adinsa na shugabancin kungiyar ya kare. Shugaban kasar Faransa Manuel Macron na daga cikin shuwagabannin kungiyar ta Francophone da suke goyon bayan shugabancin Louise Mushikiwabo.
Kungiyar kasashen renon Faransa ko masu magana da harshen turancin faransa tana da membobi 54 ne , 30 daga cikinsu a matsayin masu sa ido. Kasashen kungiyar suna da mutane kimani miliyon 900 mafi yawansu a kasashen Afrika.