Mali : Kifewar Kwale-kwale Ta Yi Ajalin Mutum 26
Ma'aikatar sufirin al'umma a Mali, ta sanar da cewa mutum 26 ne suka rasa rayukansu a yayin kifewar wasu kwale-kwale biyu a yankin Arnassey dake karamar hukumar Bourem Inaly a jihar Tombouctou.
Sanarwar ta ce an tsamo gawarwakin mutum 22 daga cikin 48 dake cikin kwale-kwalen guda biyu, a lokacin da hatsarin ya auku a ranar Asabar data gabata.
Galibin dai wandanda lamarin ya rutsa dasu manoma ne dake kan hanyar zuwa gonakinsu, a daidai lokacin da kwale-kwalen biyu suka nutse, kamar yadda wani dan kauyen ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP.
Wani wakilin talakawan yankin ya shaida cewa sun yi nasara ceto wasu mutanen.
A sanarwar data fitar ma'aikatar sufirin kasar ta gargadi jama'a akan wajabcin kiyaye dokokin yin lodi fiye da kima da kuma rubuta sunayen fasinjojin dake hawa kwale-kwale, da kuma yin la'akari da yanayin da ake ciki da kuma rigunan ceto.