Mali : Kifewar Kwale-kwale Ta Yi Ajalin Mutum 26
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33637-mali_kifewar_kwale_kwale_ta_yi_ajalin_mutum_26
Ma'aikatar sufirin al'umma a Mali, ta sanar da cewa mutum 26 ne suka rasa rayukansu a yayin kifewar wasu kwale-kwale biyu a yankin Arnassey dake karamar hukumar Bourem Inaly a jihar Tombouctou.
(last modified 2018-10-15T13:06:49+00:00 )
Oct 15, 2018 13:06 UTC
  • Mali : Kifewar Kwale-kwale Ta Yi Ajalin Mutum 26

Ma'aikatar sufirin al'umma a Mali, ta sanar da cewa mutum 26 ne suka rasa rayukansu a yayin kifewar wasu kwale-kwale biyu a yankin Arnassey dake karamar hukumar Bourem Inaly a jihar Tombouctou.

Sanarwar ta ce an tsamo gawarwakin mutum 22 daga cikin 48 dake cikin kwale-kwalen guda biyu, a lokacin da hatsarin ya auku a ranar Asabar data gabata.

Galibin dai wandanda lamarin ya rutsa dasu manoma ne dake kan hanyar zuwa gonakinsu, a daidai lokacin da kwale-kwalen biyu suka nutse, kamar yadda wani dan kauyen ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP.

Wani wakilin talakawan yankin ya shaida cewa sun yi nasara ceto wasu mutanen.

A sanarwar data fitar ma'aikatar sufirin kasar ta gargadi jama'a akan wajabcin kiyaye dokokin yin lodi fiye da kima da kuma rubuta sunayen fasinjojin dake hawa kwale-kwale, da kuma yin la'akari da yanayin da ake ciki da kuma rigunan ceto.