Moroko: "Yan Ci-Rani 38 Sun Tsira Daga Halaka
(last modified Tue, 16 Oct 2018 12:15:14 GMT )
Oct 16, 2018 12:15 UTC
  • Moroko:

Sojan ruwan kasar Moroko sun sanar da ceto da mutane 39 da suke cikin wani karamin kwale-kwale da ya kusa nutsewa a gabar ruwan garin Tanger a arewacin kasar.

Majiyar ta ci gaba da cewa daga cikin mutanen ya rasu,yayin da sauran 38 din su ka tsira.

Bugu da kari, rahoton ya ci gaba da cewa; A kowace rana ta Allah ana samun karin 'yan asalin kasar Moroko wadanda suke son ficewa daga kasar da zummar zuwa ci-rani a kasashen nahiyar turai.

A kowace shekara dubban mutane ne da su ka fito daga kasashen Afirka suke ratsawa ta Moroko akan hanyarsu ta shiga cikin kasashen turai. Sai dai da dama daga cikinsu kan halaka a cikin ruwa, ko kuma a cikin sahara.

A cikin shekarun bayan nan kasar Morokin ta zama muhimmiyar hanyar da 'yan ci-rani kan bi domin shiga cikin kasar Spaina, daga can kuma zuwa sauran kasashen turai.