'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 6 A Arewacin Mali
(last modified Sun, 21 Oct 2018 19:00:36 GMT )
Oct 21, 2018 19:00 UTC
  • 'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 6 A Arewacin Mali

Wasu 'yan bindiga kan babuta sun kai hari garin Gao dake arewacin kasar Mali tare da hallaka mutane 6

Majiyar tsaron kasar Mali ta sanar da cewa wasu 'yan bindiga dake kan babura sun kai hari garin Gao dake arewacin kasar inda suka hallaka fararen hula 6.

Rahoton ya ce har ya zuwa yanzu babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, saidai an bayyana cewa salon kai harin ya yi kama da mayakan jihadi masu da'awar kafa daular musulinci a yankin sahara.

Tun a shekarar 2012 ne yankin Gao na arewacin Mali ke fama da matsalar tsaro.

Dangane da wannan matsala, Babban kwamandan ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD dake kasar Jean-Pierre La croix, ya yiwa Kwamitin tsaron MDD bayyanin dagulewar harakokin tsaro a kasar ta Mali, musaman ma a yankunan tsakiya da arewacin kasar.