Gwamnatin Tunusiya Ta Sanar Da Rusa Wata Kungiyar Ta'addanci A Kasar
Oct 22, 2018 12:36 UTC
Ma'aikatar harkokin cikin gidan Tunusiya ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun yi nasarar rusa wata kungiyar ta'addanci a shiyar yammacin kasar ta Tunusiya.
Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Tunusiya ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun yi nasarar rusa wata kungiyar 'yan ta'adda a lardin Qasserine da ke shiyar yammacin kasar.
Sanarwar ta kara da cewa: Jami'an tsaron Tunusiya sun jima suna bibiyar kai komon gungun 'yan ta'addan, inda bayan gano yawansu tare da mafakarsu suka farmusu tare da halaka da dama daga cikinsu.
Har ila yau jami'an tsaron kasar ta Tunusiya sun yi nasarar halaka manyan kwamandojin kungiyar ta ta'addanci da ake nemansu ruwa ajallo.
Tags