An Kashe Sojojin Tawagar MDD Biyu A Mali
Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali (Minusma), ta sanar da mutuwar sojojinta biyu da kuma raunanar wasu biyar a wasu jerin hare hare da aka kai a arewaci da kuma tsakiyar kasar Mali.
Bayanai daga kasar sun ce wasu motoci ne dauke da muggan makamai ciki harda na roka suka kai harin da sanyin safiyar yau Asabar, a yankin Ber dake jihar Tumbuktu a arewacin kasar ta Mali.
Koda yake sanarwar bata bayyana sojojin da lamarin ya rusa dasu ba, amma wata sanarwa da rundinar sojin kasar Burkina Faso ta fitar ta ce sojinta biyu dake cikin tawagar Minusma sun mutu a yankin Ber da kuma wasu biyar da suka raunana.
Harin na biyu wanda aka kai da wani abun fashewa an kai shi ne a lardin Konna dake jihar Mopti a tsakiyar kasar.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da sojojin tawagar wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya ( Misnusma) ke fuskantar hare hare daga mayakan dake ikirari da sunan jihadi a tsakiya da kuma arewacin kasar ta mali ba.