Majalisar Kungiyar Kasashen Larabawa Ta Yi Allah Wadai Da Harin Tunisiya
(last modified Tue, 30 Oct 2018 12:14:13 GMT )
Oct 30, 2018 12:14 UTC
  • Majalisar Kungiyar Kasashen Larabawa Ta Yi Allah Wadai Da Harin Tunisiya

Shugaban Majalisar kasashen larabawan Mashal Bin Fahm Al Salami ya bayyana cewa; Majalisar tana yi wa gwamnati da majalisar dokokin Tunsiya juyayin abin da ya faru na harin kunar bakin waken da aka kai

Bugu da kari ya ce; Majalisar ta kasashen Larabawa tana mai jaddada goyon bayanta ga jami'an tsaron kasar a kokarin da suke yi na tabbatar da tsaro.

A jiya Litinin ne wata mace da ta yi jigida da bama-bamai ta tarwatsa kanta a tsakiyar birnin kasar kusa da ginin ma'aikatar harkokin cikin gida.

A kalla mutane 15 ne su ka jikkata sanadiyyar harin, 10 daga cikinsu 'yan sanda.

Majiyar 'yan sanda ta ce binciken farko ya tabbatar da cewa matar tana da alaka ne da kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh.