Kasar Somaliya Na Fuskantar Barazanar Cutar Kwalara
Hukumar lafiya ta duniya ta ce yankuna da dama na kasar Somaliya suna fuskantar barazanar yaduwar cutar kwalara
Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin ya ambato majiyar hukumar lafiya ta kasa da kasa tana cewa; Daga tsakanin 15 zuwa 21 ga watan Oktoba an sami bullar cutar kwalara har sau 32 a fadin kasar wacce kuma ta yi sanadiyyar mutuwar mutum guda.
Yaduwar cutar kwalara a kasar ta Somaliya ta fara ne tun daga watan DIsamba na 2017 wacce ta ci gaba har zuwa yanzu. A wannan tsakanin mutane dubu shida da dari hudu da tas'in da takwas ne su ka kamu da cutar, yayin da wasu 43 su ka mutu.
Hukumar lafiyar ta kasa da kasa ta yi kira ga ma'aikatan lafiya na kasar da su zage damtse wajen fuskantar taduwar cutar.