Kamaru : An Rantsar Da Paul Biya A Wa'adin Mulki Karo na 7
Nov 06, 2018 17:20 UTC
Shugaba Paul Biya na kasar Kamaru ya yi rantsuwar kama aiki a wani wa'adin mulki karo na bakwai.
Hakan dai zai baiwa Mista Biya ci gaba da mulkin kasar ta Kamaru har na tsawan akalla shekara 43.
A jawabin rantsar dashi shugaba Paul Biya ya yi kira ga masu fafatukar ballewa a yankin masu magana da harshen turancin Ingilishi dasu ajiye makaman yaki.
Bikin rantsar da shugaban kasar na zuwa ne kwana guda bayan sace mutane 82 da suka hada da dalibai 79 a yankin.
Yankunan yammaci da kuma kudu maso yamma na kasar ta Kamaru na dai fama da tashe tashen hankula.
Daruruwan fararen hula ne suka kaucewa muhallansu a yankunan.
Tags