Mali : Barazanar Mayakan Jihadi Ta Hana Yara 2,000 Zuwa Makaranta
(last modified Tue, 06 Nov 2018 18:18:25 GMT )
Nov 06, 2018 18:18 UTC
  • Mali : Barazanar Mayakan Jihadi Ta Hana Yara 2,000 Zuwa Makaranta

Wakilan jama'a a arewa maso gabashin ksar Mali sun ce kimanin dalibai 2,000 ne barazanar mayakan dake ikirari da sunan jihadi ta hana zuwa makaranta yau sama da mako guda.

Mayakan na kuma cilasta koyar da yara karatun addini kawai.

Wani malamin makaranta a yankin da ya bukaci kamfanin dilancin labaren AFP ya sakaya sunansa ya shaida cewa mayakan sun zo kan babura a kauyukan yankin inda suka rufe duk makarantun boko suka tara jama'a a masallatai tare da koyar da jama'a karatun al'kur'ani.

Sun kuma sha alwashin hukunta duk wanda ya ki bin sabuwar dokar.

Ana danganta mayakan da na malamin nan Amadu Kufa mai tsatsaran ra'ayi, wanda ya kafa kungiyarsa shekara uku da suka gabata a tsakiyar kasar ta Mali.

Wata majiyar tsaro ta shaida cewa tuni gwamnatin Mali ta aike da sojoji domin tabbatar da doka da oda da kuma kare lafiyar al'ummar yankin da dukiyoyinsu.