Kotu Ta Dage Shari'ar Malam Zakzaky Har Zuwa 22 Ga Watan Janairu
Kotun da ke shari'a wa Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, jagoran harkar Musulunci a Nijeriya ta dage sauraren karar da aka gabatar a gabanta har sai zuwa ranar 22 ga watan Janairun 2019 don fara shari'ar, kamar yadda kuma ta yi watsi da batun ba da belinsa da lauyoyinsa suka bukata.
Rahotanni daga jihar Kadunan sun bayyana cewar a safiyar yau ne aka gabatar da Sheikh Ibrahim El-Zakzaky din tare da mai dakinsa malama Zeenatu Ibrahim a gaban kotun don sauraren hukuncin da alkalin kotun zai yanke dangane da bukatar da lauyoyin Sheik Zakzaky din suka gabatar na a ba da belinsa, inda daga karshe dai ya ki amincewa da batun ba da belin sai dai ya ba da umurnin a gaggauta fara shari'ar, yana mai sanya ranar 3 ga watan Disamba a matsayin ranar da za a fara shari'ar, to sai bisa bukatar da Sheik Zakzaky din ya gabatar, an tsayar da ranar 22 ga watan Janairun 2019 don fara shari'ar inda lauyoyin gwamnati za su fara gabatar da shaidunsu.
Kafin hakan dai rundunar 'yan sandan jihar Kadunan ta dau tsauraran matakan tsaro a garin musamman yankin da kotun yake don guje wa duk wani abin da zai iya faruwa a lokacin da za a gabatar da Sheikh din a gaban kotun.
Tun a shekara ta 2015 ne dai mahukuntan Nijeriya din suke tsare da Sheikh Zakzaky bayan wani hari da suka kai gidansa da kuma tafiya da shi tare da mai dakin nasa, inda har ya zuwa yanzu ake ci gaba da tsare shi duk kuwa da umurnin da kotu ta bayar na a sake shi.