Ebola : WHO Ta Yi Kira A Girke Sojoji A Jamhuriyar D. Congo
Nov 09, 2018 10:22 UTC
Hukumar lafiya ta Duniya WHO, ta yi kira da a girke sojoji a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo don karfafa sha'anin tsaro a yayin da kasar ke fama da barazanar cutar Ebola.
Shugaban hukumar ne Tedros Adhanom ne ya bayyana hakan, inda ya ce cutar na ci gaba da yin barazana ga rayuwar jama'a.
Shi ma dai babban mai kula da ayyukan jin kai na MDD Jean-Pierre Lacroix, ya yi irin wannan kiran, inda ya yi fatan za a shawo kan matsalar tsaro a kasar musamman a birnin Beni dake zaman cibiyar cutar Ebola.
Tun bayan sake barkewar cutar ta Ebola a wannan kasa ta Dr Congo, sama da mutane 300 ne suka kamu da cutar, a yayin da ta kuma yi ajalin mutane kimanin 190.
Tags