An Dage Zaben 'Yan Majalisar Dokoki A Chadi
(last modified Tue, 13 Nov 2018 06:19:42 GMT )
Nov 13, 2018 06:19 UTC
  • An Dage Zaben 'Yan Majalisar Dokoki A Chadi

A Chadi, an dage zaben 'yan majalisar dokokin kasar da ya kamata a gudanar dashi a cikin wannan wata na Nuwamba da muke ciki.

Wani jami'i a hukumar shiga tsakanin harkokin siyasa ta kasar (CNDP) mai suna Abdramane Djasnabaille,  ya shaida wa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, sun yanke shawarar dage zaben har zuwa watan Mayu na shekarar 2019 mai zuwa.

A watan Afrilu da ya gabata ne shugaban kasar ta Chadi, Idriss Déby Itno, ya sanar da dage zaben 'yan majalisar dokokin kasar har zuwa watan na Nuwamba.

Kuma tun a lokacin ne hukumar ta CNDP data kunshi mambobi 15 na bangaren masu mulki da kuma 15 daga 'yan adawa ke tattauna yadda za'a shirya kundin zaben da kafa hukumar zaben kasar mai zaman kanta.

Marabin da a gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki a kasar Chadi tun shekara 2011.

Wasu dai na danganta dage zaben da matsarlar tsaro da kuma rashin kudi.