Najeriya : Boko Haram Ta Kai Wa Sansanonin Soji uku Hari
(last modified Mon, 19 Nov 2018 17:11:35 GMT )
Nov 19, 2018 17:11 UTC
  • Najeriya : Boko Haram Ta Kai Wa Sansanonin Soji uku Hari

Rahotanni daga Najeriya na cewa, 'yan ta'addan Boko haram sun kai wa sansanonin soji uku hari a yankin arewa maso gabashin kasar a cikin mako guda.

Wata majiyar tsaro ta shaidawa kamfanin dilanci labaran AFP cewa, a ranar Lahadi data gabata mayakan kungiyar da aka fi sani da Boko Haram, sun kai hari a wani sansanin soji dake Metele wani kauye dake da 'yar tazara da iyaka da kasar Nijar inda suka kori sojoji, koda yake daga baya sojojin sun sake kwace sansanin bayan samun dauki.

Haka kuma a cewar labarin, a ranar ta Lahadi mayakan sun kai hari a wani sansanin soji a garin Gajiram, dake nisan kilomita 80 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Dama a ranar Asabar data gabata mayakan sun kai hari a kauyen Mainok, inda suka kashe wani soja guda tare da awan gaba da wata babbar mota ta mayakan sa kai dake taimaka wa sojoji a yaki da kungiyar ta Boko Haram.

Tuni dai aka fara nuna fargaba akan yawaitar hare haren kungiyar musamman a daidai lokacin da aka kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa dana 'yan majalisar  tarayya a wannan kasa ta Najeriya.