An Sace Wasu 'Yan Masar 6 A Libiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34191-an_sace_wasu_'yan_masar_6_a_libiya
Rahotanni daga Libiya na nuna wasu 'yan bindiga sun sace wasu ma'aikata 'yan asalin kasar Masar 6 a gabashin Libiya.
(last modified 2018-11-22T10:27:17+00:00 )
Nov 22, 2018 10:27 UTC
  • An Sace Wasu 'Yan Masar 6 A Libiya

Rahotanni daga Libiya na nuna wasu 'yan bindiga sun sace wasu ma'aikata 'yan asalin kasar Masar 6 a gabashin Libiya.

Mazauna yankin dai sun danganta sace ma'aikatan da daukan fansa, saboda matsalar kudi.

Lamarin dai ya hadassa fargaba a zukatan dubban Misrawa dake aiki a kasar ta Libiya.

Wasu majiyoyi daga yankin sun ce uku daga cikin ma'aikatan da aka sace sun samu tsarewa daga hannun 'yan bindigan, amma babu tabas akan inda ake tsare da mutanen.