Nijar : Boko Haram Ta Kashe Ma’aikatan Man Fetur 7 A Diffa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34194-nijar_boko_haram_ta_kashe_ma’aikatan_man_fetur_7_a_diffa
Rahotanni daga jamhuriya NIjar na cewa wasu ‘yan bindiga da ake dangata cewa na kungiyar Boko Haram ne, sun kashe ma’aikatan kamfanin Foraco 7 da ke aikin hakar rijiyoyin mai a garin Toumour da ke jihar Diffa a gabashin kasar.
(last modified 2018-11-22T12:24:07+00:00 )
Nov 22, 2018 12:23 UTC
  • Nijar : Boko Haram Ta Kashe Ma’aikatan Man Fetur 7 A Diffa

Rahotanni daga jamhuriya NIjar na cewa wasu ‘yan bindiga da ake dangata cewa na kungiyar Boko Haram ne, sun kashe ma’aikatan kamfanin Foraco 7 da ke aikin hakar rijiyoyin mai a garin Toumour da ke jihar Diffa a gabashin kasar.

Mayakan sun zo ne kan dawakai a cewar labarin, inda kuma suka jikkata mutum bakwai.

Bayanai daga yankin sun ce lamarin ya auku ne sanyin safiyar yau Alhamis, kuma mayakan sunyi awan gaba da motocin kamfanin na Foraco mallakin Faransa guda biyu, kafin daga bisani su janye su nufi kudancin Najeriya dake makobtaka da kasar.