An Rage Albashin Manyan Jami'an Gwamnati A Zimbabwe
(last modified Fri, 23 Nov 2018 04:04:35 GMT )
Nov 23, 2018 04:04 UTC
  • An Rage Albashin Manyan Jami'an Gwamnati A Zimbabwe

Gwamnatin Zimbabwe ta dauki matakin rage albashin manyan jami'an kasar da kashi biyar cikin dari.

Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin ministan kudi na kasar, a lokacin da yake gabatar da kasafin kudin kasar na farko na mulkin shugaba Emmerson Mnangwa.

Ko baya ga wannan matakin da zai fara aiki daga watan Janairu na 2019, an dauki matakin tantance ma'aikatan gwamnati ta hanyar na'ura domin gano ma'aikatan bogi.

Duka wadanan matakan na daga cikin kokarin da gwamnatin kasar ke yi na farfado da tattalin arzikin kasar da ya durkushe.

Kasafin kudin kasar na 2019 dai ya tasa Dala Biliyan 6,6 wanda kuma ya kunshi biyan diyya ta Dala miliyan 53 ga manoma fararen fata da aka kora daga gonnakinsu a lokacin gwamnatin tsohon shugaba Robert Mugabe.