Nov 24, 2018 19:20 UTC
  • Fadan Kabilanci Ya Ci Rayukan Mutane 8 A Kasar Chadi

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato majiyar tsaron kasar na cewa; An kai hari ne a garin Champole da ke gabacin kasar ta Chadi kuma maharan ranci na kare

A cikin watan Oktoba ma wasu maharin sun kashe mutane da dama a wani fada na kabilanci da ya afku a garin Abeche.

Ana samun fadan kabilanci akai-akai a cikin kasar ta Chadi wanda bisa rinajiye yake cin rayukan mutane.

Bayan ga rikicin kabilanci Chadin na fuskantar hare-hare daga kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram wacce take da cibiya a kasashen da suke bakin tafkin Chadi.

Tags