Sudan: Jam'iyyun Siyasa Sun Nuna Rashin Amincewarsu Da Kulla Alaka Da Isra'ila
(last modified Mon, 26 Nov 2018 05:35:46 GMT )
Nov 26, 2018 05:35 UTC
  • Sudan: Jam'iyyun Siyasa Sun Nuna Rashin Amincewarsu Da Kulla Alaka Da Isra'ila

Jam'iyyun siyasa da dama a kasar Sudan sun nuna rashin amincewarsu kan hankoron da gwamnatin kasar take yi an neman kulla alaka da Isra'ila.

A wani zaman taro da jam'iyyun siyasa suka gudanar a birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan a jiya, domin nuna goyon baya ga al'ummar Palastine, jam'iyyun sun kara jaddada matsayinsu na kin amincewa da duk wani yunkuri da gwamnatin kasar ta Sudan take na neman kulla hulda ta difomasiyya da Isra'ila.

Almu'iz Abbas babban daraktan cibiyar taimakon al'ummar Palastinua  Sudan, a  lokacin da yake gabatar da jawabinsa a gaban taron ya bayyana cewa, duk wani yunkuri da gwamnatin Umar Hassan Albashir take na neman kulla hulda da gwamnatin yahudawan Isra'ila ba abu ne da za su amince da shi ba.

Ya kara da cewa; kullla hulda da Isra'ila a lokacin da take ci gaba da kashe al'ummar Palastine da mamaye musu yankuna da kuma keta alfarmar wurare masu tsarki da ke Palastine, hakan yana a matsayin cin amanar al'ummar musulmi da larabawa ne baki daya.