Burkina Faso : Janar Diendere, Ya Gurfana Gaban Kotu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34241-burkina_faso_janar_diendere_ya_gurfana_gaban_kotu
A Burkina faso yau ne, Janar Gilbert Diendere, ke bayyana a gaban wata kotun sojin Ouagadugu, bisa zargin yunkurin juyin mulkin 2015.
(last modified 2018-11-26T10:19:39+00:00 )
Nov 26, 2018 10:19 UTC
  • Burkina Faso : Janar Diendere, Ya Gurfana Gaban Kotu

A Burkina faso yau ne, Janar Gilbert Diendere, ke bayyana a gaban wata kotun sojin Ouagadugu, bisa zargin yunkurin juyin mulkin 2015.

Ana dai zargin Janar Diendere da cin amanar kasa, da kisa a yayin yunkurin juyin mulkin da ya yi sanadin mutuwar mutum 14 da kuma raunana 270.

Tun a farkon watan Fabrairu ne akayi tsammanin za'a gurfanar dashi a gaban kotun. 

Ko baya ga Janar din akwai wasu mutum kimanin talatin da su ma ake tsare dasu bisa zarginsu da hannu a yunkurin juyin mulkin da baiyi nasara ba.