An Kai Harin Ta'addanci A Babban Birnin Kasar Somaliya
(last modified Tue, 27 Nov 2018 06:51:23 GMT )
Nov 27, 2018 06:51 UTC
  • An Kai Harin Ta'addanci A Babban Birnin Kasar Somaliya

"Yan sandan kasar ta Somaliya ne su ka sanar da mutuwar mutane da dama sanadiyyar harin ta'addancin da aka kai a babban birnin kasar Magadishu

Kamfanin dillancin labarun Reuters ya ambato wani jami'in 'yan sandan kasar ta Somaliya, Muhammad Hussain yana cewa; Wata mota da aka makare da bama-bamai ce ta tarwaste a kusa da wani shago da ke kasuwa a unguwar Wadajir a kudancin birnin magadishu.

Rahoton ya kara da cewa mutane 8 sun kwanta dama, yayin da wasu karin 10 su ka jikkata. Har ila yau, harin ya yi sanadin lalata shaguna da dama

Kungiyar al-shabab mai dauke da makamai kan kai hare-hare irin wadannan a cikin kasar ta Somaliya.

Tun faduwar gwamnatin shugaba Muhamma Siad Barre a 1990's kasar Somaliya ta fada cikin rashin tabbaci da tsaro. Kungiyar al-Shabab tana a matsayin babbar barazanar tsaro  ga kasar da kuma sauran kasashen makwabta