Kasashen Afirka Sun Jaddada Muhimmanci Aiki Tare Wajen Fada Da Ta'addanci
Kasashe mahalarta taron kasa da kasa kan fada da ta'addanci da aka gudanar a kasar Aljeriya sun jaddada wajibcin aikin tare musamman a tsakanin kasashen Yammacin Afirka a matsayin babban abin da zai kawo nasara a fadar da ake da ta'addanci.
Kamfanin dillancin labaran Iran IRNA ya bayyana cewa a yau Talata ce aka bude taron kasa da kasa kan fada da ta'addanci karo na biyu a birnin Algiers babban birnin kasar Aljeriya da nufin tattauna hanyoyin da za a karfafa kasashen Yammacin Afirka a fadar da suke yi da ta'addanci.
A yayin taron na kwanaki biyu dai wanda ya sami halartar wakilai 30 daga kasashen Afirka, Asiya, Turai da Amurka da kuma kungiyoyi na kasa da kasa da 40, mahalarta taron za su yi dubi cikin yanayin tsaro a yankin Sahel da kuma Sahara ta Afirka da kuma irin rawar da kasashe da cibiyoyi na kasa da kasa za su taka wajen kawo karshen matsalar tsaro da ayyukan ta'addanci da kasashen Yammacin Afirka suke fuskanta musamman hanyoyin da za a sami kudin gudanar da wadannan ayyukan.
Bayanai dai sun nuna cewa sakamakon irin nasarorin da aka samu wajen fatattakan kungiyoyin 'yan ta'adda a kasashen Siriya da Iraki, da dama daga cikin 'yan ta'addan sun gudu sun koma wasu daga cikin kasashe da yankuna na duniya musamman kasashen Afirka.