Senegal : Macky Sall, Zai Tsaya Takara A Karo Na Biyu
(last modified Sun, 02 Dec 2018 14:54:18 GMT )
Dec 02, 2018 14:54 UTC
  • Senegal : Macky Sall, Zai Tsaya Takara A Karo Na Biyu

Wasu gungun jam'iyyun siyasa a Senegal sun tsaida shugaban kasar mai ci, Macky Sall, a matsayin dan takaran su a zaben shugaban kasar mai zuwa.

Bayanai sun nuna cewa tuni shugaba Macky Sall ya amince tsayawa takara a zaben mai zuwa na ranar 24 ga watan Fabariru 2019. 

Bayan tsaida da shi a matsayin dan takaran, Mista Sall, ya kuma yi alkawarin yin aiki tukuru domin ciyar da kasar ta Senegal a gaba, ta fuskar 'yanci da kuma demokuradiyya.

Tun a watan Afrilu na 2012 ne Macky Sall, ya kama mulki a kasar ta Senegal, bayan lashe waccen zaben shugaban kasar na 25 Maris a zagaye na biyu da kashi 65,80 %  na yawan kuri'un da aka kada, inda ya kada tsohon shugaban kasar Abdulaye Wade wanda ya samu kashi 34,20 %.