Ivory Coast Ta Karbi Shugabancin Kwamitin Tsaron MDD
(last modified Tue, 04 Dec 2018 04:43:18 GMT )
Dec 04, 2018 04:43 UTC
  • Ivory Coast Ta Karbi Shugabancin Kwamitin Tsaron MDD

Kasar Ivory Coast, ta karbi shugabancin karba-karba na kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, na watan Disamban nan.

Hakan dai ya sanya nahiyar Afrika a sahun gaba a cikin ajandar taron kwamitin sulhun MDD na watan Disamba a yayin da kasar Ivory Coast take shugabancin taron na wata guda.

Za'a gudanar da mahawara a tsakanin kasashe mambobin kwamitin sulhun MDDr game da yadda za'a gyara barnar da tashe tashen hankula suka haddasa a yayin taron a ranar Laraba, wanda zai samu halartar babban sakataren MDD Antonio Guterres da shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afrika Moussa Faki.

Taron mahawarar kwamitin sulhun zai biyo bayan mahawarar da za'a bude ne wanda za ta kunshi kasashen da ba mambobin kwamitin sulhun MDD ba ne game da yadda za'a yi hadin gwiwa tsakanin MDD da hukumomi da kungiyoyin shiyya shiyya, da nufin daukar matakan rigakafin barkewar tashe tashen hankula da warware takaddama.

Baya ga hakan kuma, kwamitin sulhun MDD zai tattauna a daura guda game da rikice rikice a kasashen Guinea Bissau, Sudan ta kudu, yankin Sahel da kuma jamhuriyar tsakiyar Afrika.