Hatsarin helikofta Ya Yi Ajalin Manyan Jami'an Sudan 5
(last modified Sun, 09 Dec 2018 14:34:37 GMT )
Dec 09, 2018 14:34 UTC
  • Hatsarin helikofta Ya Yi Ajalin Manyan Jami'an Sudan 5

Rahotanni daga Sudan na cewa wasu akalla manyan jami'an biyar ne na jihar Gedaref, suka gamu da ajalinsu a yayin wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a gabashin kasar a iyaka da kasar Habasha.

Ganau sun shaida wa kamfanin dilancin labaren AFP, cewa jirgin mai saukar ungulu ya rikito ne a lokacin da yake kokarain sauka, bayan da ya bige wata hasumiya ta sadarwa, kafin daga bisani ya kama da wuta.

Jami'an da hatsarin jirgin ya rusa dasu sun hada da gwamnan jihar, da shugaban fadarsa da shugaban ma'aikatar noma ta jihar da shugaban 'yan sanda mai rikon kwarya da kuma shugaban 'yan sanda iyakoki, a kamar yadda gidan talabijin din kasar ya rawaito.

A nasa bangare kamfanonin dilancin labarai na kasar SUNA ya rawaito cewa mutane shida ne suka mutu a hatsarin a yayin da dama da suka raunana, saidai ba tare da fayyace adadinsu ba.