Majalisar Dokokin Nijar Ta Amince Da Daftarin Kasafin Kudin 2019
(last modified Sun, 09 Dec 2018 15:24:56 GMT )
Dec 09, 2018 15:24 UTC
  • Majalisar Dokokin Nijar Ta Amince Da Daftarin Kasafin Kudin 2019

Majalisar dokoin Nijar, ta amince da gagarimin rinjaye da daftarin dokar kasafin kudin shekara 2019 da gwamnatin kasar ta gabatar mata.

'Yan Majalisa 129 ne suka kada kuri'ar amincewa da kasafin kudin na 2019, a ranar Juma'a data gabata, a yayin da 33 suka ki amincewa sai biyu da suka yi rawar kuri'arsu.

Kasafin kudin na 2019 ya tasa Biliyan 2.050.76 na kudin CFA.

A cen baya dai kungiyoyin fara hula da dama a Nijar, sun yi ta zanga zanga ta nuna rashin gamsuwa da sabuwar dokar haraji dake kunshe a kasafin kudin shekara 2018 mai shirin karewa, wanda suka ce ta fi takura wa masu karamin hali a kasar.

Lura da yadda jama’a ke ci gaba da kokawa akan yanayin tsadar rayuwar da ake ciki a kasar tun bayan kaddamar da dokar harajin 2018, ya sa wadanan kungiyoyin fararen hula a karksahin jagoracin Nouhou Arzika da Ali Idrissa da Moussa Tchangari, kiran daukacin ‘yan kasar ci gaba da nuna adawa da wannan dokar harajin.