Rikicin Kabilanci Ya Lashe Rayukan Mutane 15 A Mali
A Mali, mutum 15 ne suka rasa rayukansu a wani rikicin kabilanci a tsakiyar kasar.
Rahotanni sun nuna cewa wasu masu dauke da makamai ne na wata kabila suka farma wa fulani makiyaya a yankin.
Da yake tanbbatar da hakan gwamnan jihar Mopti, Sidi Alassane Touré, ya ce za'a kafa wani shiri na karbar makamai domin kawao karshen wannan al'amari.
A yankin dai an jima ana kai wa mayaka fulani farmaki bisa zarginsu da goyan bayan mayakan dake ikirari da sunan jihadi.
Rikicin kabilanci dai a tsakiyar kasar Mali, ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane tare da cilasta wa dubbai tsarewa daga muhallensu zuwa arewacin kasar.
A cewar MDD, jihar Mopti dake tsakiyar kasar ta Mali, ta fuskanci rikicin kabilanci mafi muni a tarihin kasar.