Masar Da Wasu Kasashen Afrika Na Atisayen Soji
Rundunar sojan kasar Masar da wasu kasashen Afirka suka fara wani atisayen soja na hadin gwiwa game da yaki da ayyukan ta'addanci.
Da yake karin haske kan atisayen, mai magana da yawun rundunar sojan kasar Masar Tamer al-Refa'i ya bayyana cewa, manufar atisayen ita ce kara karfin alakar sojojin Masar da takwarorinta na kasashen Afirka da samar da hadin kai tsakanin dakarun musamman na Afirka dake yaki da ta'addanci.
Rukunin farko na kasashen nahiyar Afirka dake yankin Sahel (CEN-SAD) da za su gudanar da atisayen da kasar ta Masar, sun hada da kasashen Sudan da Najeriya da Burkina Faso.
Wannan dai shi ne karo na farko da za a gudanar da irin wannan atisaye a kasar Masar.
Atisayen wanda za a kammala a ranar 14 ga watan Disamba, za a gudanar da shi ne a sansanin sojan Masar na Mohamed Naguib, sansani mafi girma a yankin gabas ta tsakiya da Afirka, wanda ke lardin Matruh na Bahar Rum din Masar.