"Yan Majalisar Kasar Somaliya Na Son Tsige Shugaban Kasa
Kamfanin Dillancin Labarun Anatoli na kasar Turkiya ya ba da labarin cewa; "Yan Majalisar 92 sun gabatar wa da kakakin majalisar Muhammad Musrsil Abdurrahman, bukatar ganin an tsige shugagan kasa Muhammad Abdullahi Farmaju
'Yan Majalisar dokokin na Somaliya suna zargin shugaban kasar da tsoma baki fiye da kima acikin harkokin kananan hukumomin wnada zai kai ga rushewar kananan hukumomin
Bugu da kari, ana zargn shugaban kasar da kulla yarjejeniyar sirri da wasu kasashen waje domin ba su damar amfani da tasoshin jiragen ruwan Somaliya, haka nan nada, da sauke kwamandojin soja ba tare da amincewar majalisar ministoci ba
Tuni dai shugaban kasar ta Somaliya Muhammad Abdullahi ya yi watsi da zarge-zargen da 'yan Majalisar suke yi masa
Dokokin kasar ta Somaliya sun tanadi cewa idan kaso biyu cikin uku na 'yan majalisa suka amince za su iya kiran shugagan kasa da kuma tsige shi.
Da akwai 'yan majalisa 326 a kasar Somaliya da hakan ya sa ake da bukatuwa da 'yan majalisa 217 domin tsige shugaban kasar