Ghana : Za'a Fara Amfani Da Jirage Marasa Matuka A Fannin Kiwan Lafiya
(last modified Wed, 12 Dec 2018 05:47:21 GMT )
Dec 12, 2018 05:47 UTC
  • Ghana : Za'a Fara Amfani Da Jirage Marasa Matuka A Fannin Kiwan Lafiya

Majalisar dokokin Ghana ta amince da wani kudirin dokar da zai bada damar yin amfani da jirage marasa matuka a sha'anin kiwan lafiyar al'umma.

Dokar da majalisar dokokin kasar ta amince da ita, za ta ba da damar amfani da jiragen wajen jigilar kayayyakin kiwon lafiya.

Amincewar da majalisar dokokin kasar ta yi kan wannan doka, na nufin cewa, ma'aikatar lafiyar kasar da abokiyar huldarta Zipline International Inc. za su bullo da managartan matakan da za su tabbatar da yadda za a rika jigilar muhimman kayayyakin kiwon lafiya zuwa asibitoci da sauran cibiyoyin lafiya a kan lokaci ba tare da wata matsala ba.

A cewar jami'ai da zarar komai ya kammala a shekarar da ke tafe ta 2019, kasar Ghana za ta kasance kasa ta farko a yammacin Afirka, dake amfani da tsari na jigilar kayayyakin lafiya da jirage marasa matuka.