Mali : An Cafke Mutum 4 Dake Korarin Kai hare-hare
Hukumomin leken asiri a Mali, sun sanar da cafke wasu mayaka dake ikirari da sunan jihadi su guda 4 dake shirin kai hare haren ta'addanci a yayin bukukuwan karhsen shekara.
Bayanai sun nuna cewa mutanen na kokarin kai hare hare ne a wasu mahimman cibiyoyi a kasashen da suka hada da Mali, Burkina Faso da kuma Ivory Coast.
A cewar bayannan da hukumar leken asirin mali ta DGSE, ta fitar mutanen hudu suna da alaka da tagwayen hare-haren da aka kai a ranar 2 ga watan Maris a Ouagadugu babban birnin kasar Burkina Faso, da kuma sace wata malamar Krista 'yar asalin Columbia a watan fabrairu na 2017 a Mali.
Ma'aikatar leken asirin ta Mali, ta ce yanzu haka tana aiki kafada da kafada da takwarorinta na wasu kasashen yankin domin musayar bayanai don yakar ayyukan ta'addanci da kuma tsautsaran ra'ayi.