Mali : Za'a Kara Karfafa Tsaro A Tumbuktu
Gwamnatin Mali, ta sanar da wasu sabbin matakai na karfafa tsaro a birnin Tumbuktu da gewajensa, duba da yadda matsalar tsaro ta addabi mazauna yankin.
Da yake sanar da hakan ga manema labarai, bayan wani ran gadi na kwanaki biyu da ya kai a yankin, shugaban gwamnatin kasar, Soumeylou Boubeye Maïga, ya ce za'a kara yawan jami'an 'yan sanda dana Jandarma da kuma sojoji a jihar dake arewacin kasar.
Koda yake bai bayyana takamaimai lokacin da za'a kara yawan jami'an ba, amma ya ce za'a aike da karin jami'an tsaro 350 a brinin na Tumbuktu da kuma jihar.
Ko baya ga hakan a cewar firayi ministan kasar za'a aike da karin kayan aikin soji, sannan za'a kafa wata sabuwar rundina ta jami'an tsaron iyakoki.
Yankin arewacin Mali dai na fuskantar matsalolin tsaro tun bayan da ya fada hannun mayakan dake ikirari da sunan jihadi dake da alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta Al-Qaïda a shekara 2012.