Shugaban kasar Ghana ya kori alkalai uku daga aiki
Shugaba Nana Akufo-Addo na kasar Ghana, ya kori wasu manyan alkalai uku na kotunan kasar daga bakin aiki, sakamakon sakamakon aikata laifuka masu nasaba da cin hanci da karbar rashawa.
Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta ce an kori mai shari'a Ayisi Addo, da Uter Paul Dery, da Mustapha Logoh daga bakin aikinsu, bayan samun sakamakon da kwamitin da aka kafa don binciken zargin da ake musu, wanda ya ce halayyar da alkalan suka nuna, ta sabawa dokokin kasar ta Ghana.
Babbar mai shari'a ta kasar Sophia Akuffo ce dai ta kafa kwamitin binciken, bayan da dan jaridar nan mai kwarmata bayanai Anas Aremeyaw Anas ya gabatar da korafi a kan su.
Alkalan uku dai na cikin jimillar alkalai 22, na manya da kananan kotunan kasar da aka zarga da aikata cin hanci da rashawa shekaru uku da suka gabata.