Burkina Faso : An Kasa Cimma Matsaya Kan Batun Rage Farashin Mai
(last modified Wed, 19 Dec 2018 05:27:04 GMT )
Dec 19, 2018 05:27 UTC
  • Burkina Faso : An Kasa Cimma Matsaya Kan Batun Rage Farashin Mai

A Burkina Faso, an kasa cimma matsaya tsakanin gwamnatin kasar da kuma kawacen kungiyoyin dake yaki da tsadar rayuwa kan batun rage farashin man fetur.

Yau kusan mako guda kenan da bangarorin biyu ke tattaunawa kan batun, bayan zanga-zanga da kungiyoyin fara hula dana kwadago suka shirya na bukatar rage farashin man fetur.

A watan Nowamba da ya gabata ne gwamnatin kasar ta sanar da karin kudin CFA 75, kan ko wanne lita na man fetur a gidajen shan mai, lamarin da bai yi wa wasu 'yan kasar dadi ba.

Gwamnatin kasar dai ta ce zata tuntumi kamfanonin man fetur da kuma na wutar lantarki na kasar domin duba yadda za'a samu ragowar farashin na mai kamar yadda masu zanga-zangar ke bukata.

Ministan sadarwa na kasar, Remis Fulgance Dandjinou, ya bukaci al'ummar kasar da suyi hankuri har zuwa karshen watan Janairu na shekara mai shirin kamawa, a yayin da su masu zanga zangar ke bukatar a dawo da farashin na waccen lokacin kafin ayi karin na CFA 75.