An Kashe Mutane Akalla 200 A Kasar Mali A Wannan Shekara
Majiyar rundunar tabbatar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya A Kasar Mali MUNUSMA ta bayyana cewa daga farkon wannan shekara har zuwa watan Nuwamba da ya gabata yan ta'adda sun kashe mutane 209 fararen hula a tsakiyar kasar
Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya nakalto majiyar ta MUNUSMA tana cewa daga cikin wadanda aka kashe 13 yara kananane sannan mata 7.
Labarin ya kara da cewa yan ta'adda sun kai hare-hare a wurare daban-daban a tsakiyar kasar har sau 60, sannan hare-haren an kaisu ne kan kabilar Fulani wadanda suke rayuwa a garuruwan Mpoti da kuma Segou.
Banda haka wasu mutane kimani dubu 3 ne suka kauracewa gidajensu a yankin, sannan mutane 13 kuma suka bace.
Rundunar MUNUSMA ta kammala da cewa a ranar 23-25 na watan Yunin shekarara da muke ciki kadai yan ta'adda sun kai hari a garin Komaga a yankin Mopti inda suka kashe fararenhula 24 dukkaninsi daga kabilar Fulani.