Mali : An Sanya Wa Masu Kawo Cikas Ga Yarjejeniyar Zaman Lafiya Takunkunmi
(last modified Fri, 21 Dec 2018 04:37:31 GMT )
Dec 21, 2018 04:37 UTC
  • Mali : An Sanya Wa Masu Kawo Cikas Ga Yarjejeniyar Zaman Lafiya Takunkunmi

A karon farko, Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya, ya sanya takunkumi kan wasu 'yan kasar Mali dake kawo cikas yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma tsakanin 'yan kasar a shekara 2015.

Takunkumin dai ya shafi 'yan mali guda uku, wanda ya hada da haramta masu tafiye tafiya, amma kuma akwai yiyuwar za'a kara daukan wasu matakai kansu ciki har da toshe kaddarorinsu, kamar yadda wasu majiyoyin diflomatsiyya suka tabbatarwa da kamfanain dilancin labaren AFP.

Mutanen uku sun hada da sakataren kawancen al'ummar Azawad (CPA), cewa da Mohamed Ousmane Ag Mohamedoune, da  Ahmoudou Ag Asriw, shi kuwa wani jigo a hadin guiwar Buzayen imghad na (Gatia), sai kuma Mahamadou Ag Rhissa, wani hamshakin mai kudi a majalisar koli ta hadin kan Azawad (Hcua).

Saidai wasu sun ce hakan bai zo da mamaki ba, kasancewar mutanen suna da alaka da gungun kungiyoyin 'yan ta'adda da kuma harkokin safara muggan kwayoyi.

Ana dai takunkumin hana tafiye tafiyen zai yi tasiri ga mutanen uku kasancewar suna yawan tafiye tafiye a yankin na Sahel.

Wannan dai shi ne karo na farko da MDD, ta dauki irin wannan mataki kan daidaikun mutane dake kawo cikas a yarjejeniyar ta zaman lafiya a Mali.