Dec 23, 2018 19:24 UTC
  • An Kara Dafifin Sojojin Kasar Mali A Yankunan Tsakiyar Kasar

Firai Ministan kasar Mali ya bayyana cewa gwamnatin kasar ta kara yawan sojoji da jami'an tsaron kasar a yankunan tsakiyar kasar don dawo da zaman lafiya a cikinsu.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto wannan labarin daga shafin tweeter na Firai ministan kasar ta Mali Sumai'ila Bubeye Maiga a yau Lahadi.

Maiga bai bayyana yawan sojojin da jami'an tsaron da aka kara a wadannan yankuma ba, sannan bai bayyana zuwa yauce ne zasu fara aikin kwance damarar yan bindiga a yankunan ba. 

Yankunan tsakiyar kasar Mali dai suna fama da tashe-tashen hankula na kabilanci tun shekara ta 2016, sannan majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa a cikin wannan shekara ta 2018 mai karewa kadai mutane akalla 500 ne suka rasa rayukansu a yankunan. 

Shugaban kasar Mali Ibrahim Bubakar Kaita wanda aka sake zabensa kan kujerar shugabancin kasar a zaben watan Augusta na wannan shekara ya bar Firai ministan kasar Sumaila Bubeye Maiga kan kujerarsa .

Tags