Gwamnatin Kasar Mali Na Shirin Kwance Damarar Yakin Masu Dauke Da Makamai
Pira ministan kasar ta Mali ne ya sanar da cewa; An sake aikewa da sojoji zuwa tsakiyar kasar sannan kuma an shirin kwance damarar masu dauke da makamai
Pira ministan Soumeylou Boubeye Maiga ya bayyana haka ne a wani bayani da ya wallafa a shafinsa na Twitter, sannan ya kara da cewa; Gwamnatin tana son kara tabbatar da karfinta a cikin tsakiyar wannan kasa
Pira ministan na kasar Mali bai yi wani karin bayani akan adadin sojojin da aka aike zuwa tsakiyar kasar ba, ko kuma salon aikin da za su gudanar
Tsakiyar kasar Mali tana fuskantar tashe-tashen hankula tun daga 2016. Wani rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya ce a cikin wannan shekara ta 2018 kadai an kashe mutane 500 a tsakiyar kasar ta Mali
Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya bar Soumeylou Maiga akan mukaminsa bayan sake zabensa da aka yi a matsayin shugaban kasa a watan Agusta na wannan shekara ta 2018