An Kai Hari Ma'aikatar Harkokin Wajen Libiya
Rahotanni daga Libiya na cewa mutum uku ne suka rasa rayukansu, kana wasu goma na daban suka raunana bayan wani hari da aka kai a ma'aikatar harkokin wajen kasar dake birnin Tripoli.
Wasu majiyoyin tsaro sun ce daga cikin wadanda lamarin ya rusa dasu harda wani jami'in diflomatsiyya.
Ganau sun shaidawa masu aiko da rahotanni cewa, wani harin bom ne aka kai da mota a kusa da ginin ma'aikatar, kafin daga bisani wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kanta a hawa na biyu na ginin.
A cikin wata sanarwa data fitar ma'aikatar harkokin wajen kasar ta tabbatar da aukuwar lamarin tare da dangantasa da harin kunar bakin wake na ta'addanci.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Tarak al-Dawass, ya dora alhakin harin ga kungiyar 'yan ta'adda ta (IS), tare da jinjinawa jami'an tsaron kan takaita yunkurin maharan na aikata babban ta'adi.
Kasar Libiya dai ta fada cikin matsalar tsaro ne tun bayan kifar da mulkin Muammar Ghaddafi a cikin shekara 2011, inda kasar yanzu haka ke fama da rikici tsakanin gwamnatoco biyu, ta hadin gwiwa (GNA) dake samun goyan bayan kasashen duniya dake Tripoli, da kuma wacce take a gabashin kasar da marshal Khalifa Haftar ke jagoranta.
Rikicin na siyasa dana tsaro da kasar ta fada dai ya taimakawa gungun mayaka masu dauke da makamai kusawa cikin kasar tare da kaddamar da hare hare da dama a cikin kasar.