Jan 01, 2019 15:49 UTC
  • Chadi : Za'a Gudanar Da Zabuka A Cikin Watanni Masu Zuwa_Deby

Shugaban Kasar Chadi Idriss Deby ya ce za'a gudanar da zabubukan kasar da suka hada dana 'yan majalisar dokoki da kuma na kananen hukumomi a tsakiyar wannan sabuwar shekara ta 2019.

Shugaba Deby, ya bayyana hakan ne a cikin jawabinsa na sabuwar shekara inda ya tabbatar da cewa za'a gudanar da zabukan a cikin watanni na wannan shekara.

An dai jima ana dage wadannan zabubukan a kasar ta Chadi, tun bayan wadanda aka gudanar a shekara 2011.

Ko baya ga hakan a ranr 21 ga watan Yuli na shekara 2015 ne wa'adin 'yan majalisar dokokin kasar ya kawo karshe, amma aka tsawaita wa'adinsu.

Saidai da yake maida martani kan jawabin shugaban aksar, jagoran 'yan adawa na kasar, Saleh Kebzabo, ya ce ba shugaban ne ba keda nauyin tsaida ranar zabe, don kuwa akwai hukumar da aka dorawa wannna yaunin wato hukumar zaben kasar mai zaman kanta (CENI), wacce ya kamata a gagguta kafa ta a tsakiyar wannan wata, domin ta sanar da lokutan zabe kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Daya daga cikin dalilai da gwamantin Chadi ta bayar na dage zabukan harda matsaloli na rashin kudi, saboda a cewarta faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya.

Saidai a ranar 23 ga watan Disamba da mukayi ban kwana dashi, a yayin wata ziyara a kasar Chadi, shugaban kasar Faransa Emanuelle Macron ya yi alkwarin taimakawa kasar ta Chadi domin shirya zabukanta.

Tags