Somaliya Ta Kori Wani Babban Jami'in MDD
(last modified Wed, 02 Jan 2019 08:46:56 GMT )
Jan 02, 2019 08:46 UTC
  • Somaliya Ta Kori Wani Babban Jami'in MDD

Gwamnatin Somaliya ta umurci wakilin majalisar dinkin duniya a kasar da ya fice daga kasar, bisa zarginsa da shishigi a cikin al'amuran kasar.

Matakin gwamnatin dai ya zo ne kwanaki kadan bayanb da jami'in MDD, Nicholas Haysom, ya bayyana damuwarsa kan matakan da jami'an tsaron Somaliya suka dauka na murkushe masu zanga zanga a birnin Baïdoa dake kudu maso yammacin kasar a tsakiyar watan Disamba daya shude, wanda kuma a yayinsa mutane 15 suka rasa rayukansu, kana wasu kimanin 300 suka raunana.

Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Somaliyar ta fitar ta ce bata maraba da kasancewar wakilin na MDD, a kasar kuma ba zai ci gaba da aiki a kasar ba.

Har zuwa lokacin fasara wadanan labaren tawagar MDD, a kasar ta Somliya bata maida martani kan matakin.

An dai bayyana, Nicholas Haysom, wanda aka nada shi a matsayin wakilin MDD a wannan kasa ta Somaliya a watan Satumba na 2018, a matsayin kwararen jami'in diflomatsiya. 

Dama dai ya taba rike irin wannan mukami na kasashen Sudan da Sudan ta Kudu.