Mali : An Kashe Mutum 37 A Kauyen Koulogon
Hukumomi a kasar mali sun sanar da cewa mutum 37 ne da suka hada da mata da yara suka rasa rayukansu a wani da aka kai masu a kauyen Koulogon, dake tsakiyar kasar.
A sanarwar data fitar gwamnatin kasar ta ce mutanen sun rasa rayukansu a wani hari da wani masu dauke da makamai suka kai da safiyar ranar Talata.
Rahotanni daga yankin sun ce maharan wandanda mafarautan dozo ne sun je kauyen ne kan babura da jijibin jiya Talata inda suka bude wuta kan jama'a.
Daga cikin mutanen da aka kashe harda shugaban kauyen, an kuma kone gidaje da dama.
Wasu majiyoyi daga kauyen sun bayyana cewa maharan na dauke da muggan makamman yaki.
Bayanai sun ce dama an jima da shugaban kauyen na Koulogon ke samun barazana.
Yankin tsakiyar Mali dai ya jima yana fuskantar rikice rikice masu nasaba da kabilaci.