Jan 03, 2019 04:00 UTC
  • Sojojin Nijar Sun Hallaka 'Yan Boko Haram 287 A Yankin Tafkin Chadi

Rundinar sojin kasar Nijar ta kaddamar da wani gagarimin farmaki data kai kan 'yan ta'addan boko haram a yankin tafkin Chadi, inda ta hallaka 287 daga cikinsu a cewar wata sanarwa da ma'aikatar tsaron kasar ta fitar a jiya Laraba.

Sanarwar ta ce farmakin na sama dana kasa da sojojin kasar suka kai a kudu maso gabashin kasar, a yayinsa an hallaka mayakan dake ikirari da sunan jihadi na Boko haram 200 a harin sama, sai kuma wasu 87 a kasa.

Harion wanda aka kaddamar a ranar 28 ga watan Disamba, an kai shi ne a kusa da kogin ''Komadugu'' dake cikin dajin dake raba iyaka da Najeriya da Nijar da kuma tafkin Chadi.

Ma'aikatar ta ce babu wata hasara rayuka ko kuma barna da aka samu daga bangaren sojin kasar.

Haka zalika an kuma kwato kayayakin yaki da suka hada da manya da kananan bindigogi ciki harda na harba rokoki kirar RPG, da dubban harsashai iri daban daban da wayoyin hannu na 'yan boko haram din, tare da lalata wasu kayayakinsu da suka hada da kwale kwale guda takwas.

Daga cikin kayayakin da aka kwato kuwa harda motoci guda uku da suka hada da motar wani kamfanin ginar rijiyoyi na wani kamfanin faransa mai suna Foraco da aka sace a wani harin mayakan a ranar 22 ga watan Nuwamba na shekara data shude a garin Toumour. 

Wannan farmakin dai na zuwa ne wata guda bayan da rundinar sojin kasar ta Nijar ta sanar cewa tana da fargaba akan hare hare da mayakan na Boko haram zasu kai kan sansanonin sojinta a yankin a cikin shekara 2019.

Mahukuntan Yamai dai sun ce sun damu matuka akan abunda ke faruwa a makobciyar kasar Najeriya, inda kungiyar ta Boko haram ta kaddamar da hare hare kan wasu sansanonin soji, a cewar ministan tsaron kasar Kalla Moutari, a wani bayyaninsa a zauren majalisar dokokin kasar a farkon watan Disamban da ya gabata.

Ministan ya kara da cewa, duba da yadda a watan Janairu ruwa ke ragewa a kogin Komadugu, akwai barazanar 'yan boko haram suka kai hari kan sansanonin sojin kasar, wanda a cewarsa dama ruwan ne ke hana mayakan na boko haram tsallakawa cikin kasar.

 A wani taro da shugabbanin kasashen yankin tafkin na Chadi wanda suka hada da Najeriya, Nijar, Chadi da Kamaru suka gudanar a birnin N'Djamena na kasar Chadi a ranar 29 ga watan Nuwamba na shekara data gabata, bangarorin sun bukaci taimakon kasa da kasa kan yakin da suke da kungiyar ta Boko Haram.

Shuwagabannin kasashen da suka hada da Muhammadu Buhari na Najeriya, Mahammadu Isufu na Nijar, da Idriss Deby Itmo na Chadi da kuma shugaban gwamnatin Kamaru wandanda kasashensu mambobin kwamitin tafkin Chadi, na (CBLT), ne sun sha alwashin ganin bayan kungiyar Boko haram domin kawo karshen tsatsauran ra'ayi a yankin.

A sanarwar karshen taron da suka gudanar, shuwagabannin sun jaddada ci gaba da matakan da suka dauka na murkushe matsalar tsaro mai nasaba da Boko Haram a yankin tafkin na Chadi.

Taron ya kuma yaba wa kwamitin tsaro na kungiyar tarayyar Afrika (AU) kan sabunta wa'addin aikin rundinar hadin gwiwa ta kasashen yankin kan yaki da kungiyar ta Boko Haram na shekara nan ta 2019. 

Haka zalika shuwagabanin kasashen sun bayyana sahihiyar godiya ga abokan huldarsu da kuma kasashen duniya kan tallafin da suke basu akan yaki da tsatsauran ra'ayi na kungiyar Boko Haram.

Tags